A ƙoƙarinta na ganin ta shawo kan malaman jami’a don janye yajin aikin da su ke yi, gwamnatin tarayyar ta fara biyan haƙƙonkinsu malaman jami’a a Najeriya.

Shugaban ƙungiyar malaman jami’a ta ƙasa reshen jami’ar Minna a jihar Neja ne ya tabbatar wa da jaridar Punch hakan ya ce an fara biyan wasu basuka da malaman ke bin gwamnatin.
Dakta Gbolahan Bolarin ya ce an fara biyan haƙƙoƙin wasu daga cikin malaman jami’a da malaman kwalejin fasa da su ke tsaka da yajin aiki.

