Babban Bankin Najeriya, CBN, ya ce nan ba da daɗewa za a nemi naira ta takarda a rasa, yana mai shawartar mata da maza ƴan kasuwa su yi rajista da e-Naira.

kwantrola na CBN reshen Jihar Delta, Mr Godwin Okafor, ne ya furta hakan a ranar Juma’a a fitacceyar kasuwar Ogbogonogo yayin wayar da kan ƴan kasuwa game da e-Naira.
Okafor ya buƙaci ƴan kasuwan su shiga tsarin babban bankin Najeriya na e-Naira.

Ya bayyana cewa:

“Mun zo nan kasuwa ne domin wayar da kan mutane game da amfani da e-Naira.
CBN ta amince da shi, ba kamar Bitcoin da doka bata amince da shi ba.”
Kwararre na CBN kan e-Naira, Dr Aminu Bizi, ya ce an zaɓi Delta a matsayin jiha ta biyu domin wayar da mata ƴan kasuwa kan e-Naira bayan Jihar Legas.
“Mun zo nan ne domin wayar da kan maza da mata ƴan kasuwa, shago zuwa shago kan amfani da e-Naira.
CBN ta wuce da batun ATM, POS, don haka za mu wayar da kan ƴan acaba/adaidaita kan wannan sabon tsarin.
“Nan da ƙanƙanin lokaci za a dena ganin takardar Naira domin CBN na kashe kuɗi don buga ta kuma mutane suna cin zarafinta a kasuwa, liki wurin biki/taro, biyan ƴan acaba/adaidaita da sauransu, CBN na asara.”
Ya ce e-Naira yana da daɗin amfani, babu caji kamar ATM ko POS kuma ba za a iya mata kutse ba.
A jawabinsa, sakataren gwamnatin jihar, Cif Patrick Ukah, ya yaba wa CBN bisa ɓullo da tsarin na e-Naira.