Da misalin ƙarfe 1 na rana muka ɗauki hanya da nufin zuwa ƙananan hukumomin makoɗa, dawakin tofa, da Ɗanbatta daga can kuma za mu ƙetara har kazaure a jihar jigawa.
Da ike aikin da muka nufa shi ne ɗakko bayanan abin da ke faruwa don wallafawa a mujalla, tare da bawa wasu kafafen yaɗa labarai na Rediyo bayanan da muka samu kai tsaye.
Da nufarmu wani gari da ake kira ɗandalama muna zarara gudu a mota ganin ba kowa kuma muna so mu cimma ganin abinda ke faruwa a wuraren da ake yin zaɓe, caraf a hannuna na hagu na hango wasu mutum biyu a kan babur sun ɗakko akwatin zaɓe suna sharara gudu.
Nan take na taka birki ina faɗawa abokan tafiyata cewar akwatin zaɓe nw fa, a nan ne fa na juya mota na lula da gudu don cimmusu.
Wasu mutane da je kan babura aun ga abin da ya faru suma suka tiso bayanmu muna bin waɗannan mutum biyu da ke ɗauke da akwatin zaɓe.
Tun tuni dama na kira kafar yaɗa labarai ta rediyo da nake bawa bayanai kai tsaye na sanar musu, sai dai a lokaci ba a sadani da masu sauraro ba, sai na nufi mutanen don ƙara tabbatarwa.
Tsabagen gudu na kusa cimmusu suka waigo suka gammu suka fahimci su muke bi, sai suka ƙara mannewa da gudu, a nan ne na fara tunanin to idan mutanen nan suna ɗauke da makami fa? Tunda ba yadda za a yi mutum ya ɗakko akwatin zaɓe ya biyo titi ba tare da ya tanadi wani abu na kare kansa ba.
Nan dai na tuno wasu dabaru na manema labarai na bisu har na sha gabansu na wucesu.
Na kuma lailayo motata na tinkaresu sai na ga sun tsaya a wata mazaɓa da ake yin zaɓe, mutanen da suka biyo bayanmu ma suka tsaya, ɗaga idanuna da zan yi sai na hango tsire ne a cikin akwatin zaɓen, tare da takardar da yake ƙunsawa mutane, ashe sauri yake kar a watse bai siyar da naman nasa ba.
A haka na haƙura muka tafi don gujewa ɓata lokaci, wannan shi ne abin da ya faru.
Mutanen da muke tare akwai
Ibrahim Bala
Idris ya u
Fadila sani shu aibu
Zahradden Abubakar Musa
Sai kuma ni
Abubakar Murtala Ibrahim
12/03/2019


