Wasu da ake kyauta zaton ƴan bindiga ne sun hallaka shugaban hukumar ƙidaya a Najeriya tare da yin awon gaba da ƴaƴansa.

An hallaka Zakari Umaru-Kingbu a jihar Nassarawa tare da yin garkuwa da ƴaƴansa guda biyu mata.

Al’amarin ya faru a safiyar yau Lahadi yayin da ƴan bindigan su ka isa gidan sa da ke Azuba Bashayi ta Lafiya babban birnin jihar.

Marigayin na da shekaru 60 a duniya sannan tsohon ma’aikaci ne a hukumar sojin sama ta Najeriya.

Wani daga cikin ƴan uwansa ya tabbatar da cewar ƴan bindigan sun buƙaci a basu kuɗi naira miliyan 50 kafin sakin ƴaƴan nasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: