Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Litinin 13 ga watan Yunin shekarar 2022 a matsayin ranar hutu domin bikin ranar Demokradiyya ta wannan shekarar.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya a cikin wata sanarwa da ya raba wa kafafen watsa labarai a ranar Alhamis.
Ministan ya taya yan Najeriya murnar bikin ya kuma bukaci dukkan yan kasar su mara wa gwamnati mai ci a yanzu baya don tabbatar da tsaro da hadin kai da cigaba a kasar.

Ministan ya ce a yayin da ake bikin Ranar Demokradiyya a tarihin Najeriya, a kan yi waiwaye kan kokarin da mazan jiya su ka yi don tabbatar da hadin kan Najeriya a matsayin kasa daya dunƙulalliya.

Ministan ya kuma shawarci yan Najeriya su yi amfani da manhajar inganta tsaron cikin gida na (N-Alert) da aka kirkira don inganta tsaro da kare fitintunu.
Sannan ya bayar da tabbacin cewa kokarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi na tabbatar da tsaro da kawo cigaba da daidaita tattalin arziki zai ci gaba a wannan lokaci.