Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da gwmnonin jam’iyyar APC yau a fadarsa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Ganawar na zuwa ne yayin da jam’iyyar APC ke ƙoƙarin fitar da mataimakin shugaban ƙasa bayan an yi zaɓen fidda gwani.

Gwamnonin jam’iyyar APC sun halarci taron ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu.

Zaman da shugaban ya yi da gwamnonin APC akwai wasu daga cikin mukarraban gwamnatinsa kamar shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Ibrahim Gambari da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha.

Sannan gwamnonin APC na jihar Kaduna, Jigawa, Plateau, Nassarawa da Imo sun halarci zaman.

Haka kuma akwai gwamnonin jihohin Borno, da gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma.

A na zargin zaman ya duba yiwuwar saka ministan shari’a Abubakar Malami ko ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika a matsayin mataimakin shugaban Najeriya.

Jam’iyyar APC da sauran jam’iyyun siyasa a Najeriya sun mayar da hankali wjen fitar da wanda zai zama mataimakin shugaban ƙasa a yayin da ya rage kwanaki uku hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta rufe karɓar sunayen mutanen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: