Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar gano wata mata wadda ake kyautata zaton ta na daya daga cikin matan da mayakan boko haram su ka yi garkuwa da su a makarantar Sakandiren Chibok a Jihar Borno.

Rundunar ta ce ta gano matar ne a yayin da runduna ta 26 ta sojin ta ke gudanar sintiri a cikin karamar hukumar Gwoza ta Jihar.
Rundunar ta bayyana hakan ne a yau Laraba a shafin ta na Twitter.

Jami’an sojin sun bayyana cewa sun gano matar mai suna Mary Ngoshe dauke da yaro a hannun ta wanda ake kautata zaton d’anta ne.

An yi garkuwa da daliban makarantar ta Chibok ne 276 tun a shekarar 2014 da ta gabata,inda kuma aka samu nasarar tseratar da guda 100 daga wajen su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: