Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta kara wa’adin sake rufe yin rijistar katin zabe wanda a baya ta ce za a rufe yin rijistar a ranar 30 watan Yuni da mu ke ciki.

Shugaba a kwamitin majalisar wakilai bangaren zabe Hon Aisha Jibril Dukku ita ce ta tabbatar da hakan a lokacin da ta ke gabatar da jawabi ga ‘yan majalisar bisa kokarin da kwamitin ya ke yi domin tabbatar da hukuncin da su ka yanke a makon da ya gabata.
A jiya Talata ne dai kwamitin ya yi wani zama da hukumar ta INEC kuma a lokacin taron hukumar ta kara wa’adin yin katin zaben da kuma sauran wasu bukatu da kwamitin ya shigarwa da hukumar.

Majalisar wakilan ta yi hakan ne domin karawa ‘yan Najeriya wa’adin yin rijistar wanda a ranar Larabar da ta gabata kwamintin ya shigar wa da hukumar ta INEC bukatar hakan inda ta nemi da hukumar ta kara watanni biyu ga masu yin katunan zaben.

Sannan kuma majalisar ta bukaci da hukumar INEC da ta kara yawan ma’aikata da injinan yin rijistar a dukkan fadin Najeriya.