Jami’an tsaro a jihar Ondo ta kama wasu daga cikin mutanen da su ka kai hari ƙaramar hukumar Owo a jihar.

Jami’an tsaro na Amoetekun ne su ka kama mutane biyu daga cikin waɗanda ake zargi da kai hari wata coci a jihar.

Jami’an su ka ce sun ƙwato wasu makamai da ababen hawa da aka yi amfani da su wajen kai harin.

Mutane sama da 40 ne su ka rasa rayuwarsu yayin da wasu fiye da 70 su ka jikkata a harin.

Gwamnatin tarayya ta ce mayakan ISWAP ne su ka kai hari a cocin.

Gwamnatin jihar ta jiyar da ranar demokaraɗiyya da aka yi a watan da mu ke ciki domin makokin waɗanda su ka mutu.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: