Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU ta ce ba ta sa masaniya a kan wani zama da gwamnatin tarayya ta shirya yi da su yau Alhamis.

Shugaban ƙungiyar Farfesa Emmanuel Osodke ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da BBC, y ace batun da ministan ƙwadago yay i kan cewar za su zauna a y aba su da msaniyarsa.

Shugaban y ace har yanzu gwamnatin tarayya ba ta ɗauki hanyar kawo ƙarshen yajin aikin da su ke ciki ba.

Farfesa Emmanuel y ace ministan ƙadagon yay i watsi da batunsu tared da dakatar musu da albashinsu da nufin juyar da ra’ayinsu.

A jiya Laraba ministan ƙwadago a Najeriya Chirst Ngige ya shaida cewar za su zauna da ƙungiyar ASUU a yau tare da kawo ƙarshen yajin aikin.

Watanni aka shafe ɗalibai na zama a gida tun lokacin da ƙungiyar ta shig yajin aiki domin ganin gwamnatin ta waiwayesu tare da cika musu burinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: