Daga Yahaya Bala

 

Rundunar yan sandan jihar Delta ta tabbatar da hallaka wasu mutane Uku da ake zargi yan fashin ne a bayan wata fafatawa da ta auku.

Jihar Delta jiha ce wadda ke kudancin kasa Najeriya ta dade ta na fama da miyagun yan fashi yan kungiyar asiri da ma masu ta’amali da miyagun ƙwayoyi.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Bright Edafe shine ta bayyyana haka ga manema labarai inda ya ce bayan hallaka mutane Uku sun samu nasarar kama wani daga cikinsu.

Cikin Bayanin da Edefe ya yi a  jiya Lahadi a Wari ya ce an kwace dukkanin kayan wadanda ake zargin wadanda su ka hada da bindigu Babura masu kafa biyu da sauransu.

Sannan ya ce ana ci gaba da bincike akan lamarin har zuwa yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: