Shugaban kasa Mahammadu Buhari ya yi alla-wadai da kisan da masu garkuwa su ka yiiwa wani fasto bayan garkuwa da shi da suki kwanaki biyar da suka gabata a jihar kaduna.

Shugaban ya bayyana hakanne ta bakin mai taikamasa ta fannin yada labarai malam Garba Shehu ya fitar a jiya Laraba cikin wata sanarwa da ya fitar.
Buhari ya ce ya kadu matuka da kisan da aka yiwa babban malamin addinin kiristan kuma wannnan ya nuna wadanda su ka yi aika aikar mutane ne masu son tayar da hargitsi a Najeriya.

ya ce irin wadannan hare haren da yan ta adda suke kaiwa alummar da ba su ji ba su jiba ba gani ba wannnan nakasu ne ga gwamnati domin tsaro na daya daga cikin alkawarin da su ka daukawa yan kasar a lokacin yakin neman zabe.

Muhammadu Buhari ya ce kudirin sa na kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya yana nan daram kamar yadda ya dauki alkawari a farko domin cimma nasara yace yakan kira shugabanni a fanini tsaro dommin tattauna matsalar a lokaci zuwa lokaci.
Sannnan ba zai bari jamian tsaro su huta ba har sai an cimma wannan nasarar a fadin kasa Najariya.
Daga karshe ya ce ya na mai mika taaziyya ga Iyalan fasto Revran Cheitnum da kuma gwanmatin jihar kaduna da ma aluma baki daya.
An sace fasto Revran ne a kwanaki hudu da su ka gabata inda aka tsinci gawarsa a wani waje bayan an hallakashi.