Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta bayyana cewa aƙalla mutane Miliyan 11 ne su kayi rijistar zabe a ƙasar.

Kamar yadda hukumar ta sha bayyanawa a shafinta ta ce mutane miliyan 11 ne su ka kawo bayanin su aka tantance zuwa Hukumar tun fara Rijistar zuwa yanzu.

INEC ta ce mutane Miliyan 11,011,119 ne su ka yi rijista tun bayan farawa kuma mafi yawan kaso mai girma sun fito daga Jihohin Legas da Kano.

Inda Legas ke da adadin mutane da su ka yi rijista ya kai 508,936 Kano kuma na da mutane 500,207 da kuma ta ukunsu ita ce Jihar Delta mai 481,929 sai Kaduna da Rivers ke biye musu baya.

A rahoton ya nuna matasa yan shekaru 18 zuwa 34 ne suka fi yin rijistar.

Sannan mafi yawa mata ne kuma yawansu ya kai akalla miliyan 5,558,048 inda yan maza kuwa keda mutane 5,453,071 adadin wadanda su kayi rijistar zabe.

Sai dai har ya zuwa yanzu lokacin da hukumar ta INEC ta bayar na kammala zuwa yin rijistar bai cika ba wanda zai kai har ranar 31 ga watan da muke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: