Sarkin Daura Alhaji Umar Faruƙ ya auri wata Aisha Yahuza Gona mai shekaru 22 a duniya.

Ƙasa da makonni biyu da haɗuwa da ita aka ɗaura auren a gafin Safana ta jihar Katsina.

Amaryar ƴa ce ga tsohon shugaban karamar hukumar Safana Alhaji Yahuza Gona.

Tuni amaryar ta tare a gidan angonta da ke Daura kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Idan ba a manta ba, a watan Disamban shekarar da ta gabata sarkin ya auri wata Asiha Iro Maikano mai shekaru 20 a duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: