Majalisar dattawan Najeriya ta bai wa manyan hafsoshin tsaron Najeriya watanni huɗu domin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi ƙasar.

Hakan ya biyo bayan wata ganawa da majalisar ta yi da manyan hafsoshin tsaro a jiya Laraba.

Majalisar ta nuna damuwarta a kan matsalar tsaron da ke kara ta’azzara a Najeriya.

Sannan ƴan majalisar sun bai wa jam’an tsaron shawarwarin yadda za su kare birnin tarayya Abuja da sauran kasa baki ɗaya.

Kwamiti daban-daban na majalisar ya gana da shugabannin tsaron domin ganin an shawo kan matsalar.

A baya-bayan nan ne dai wasu daga cikin mambobin majalisar su ka yi yunƙurin tsige shugaban kasa bayan da su ka ce gazawarsa ta bayyana karara wajen shawo kan lamarin.

Sai dai shugaban majalisar ya yi watsi da bukatar hakan tare da yin watsi da ƙudirin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: