Shugaban  Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu daga cikin mutanen da ƴan bindiga su ka sace a cikin jirgin ƙasa Abuja zuwa Kaduna.

Muhammadu Buhari ya gana da mutanen ne bayan sakin wasu iyalai su shida da waata mata a ranar Laraba.

Daga cikin mutanen da ƴan bindigan su ka saki har da mata da ƙananan yara.

Daga ciki akwai wata Aisha Hassan mais hekaru 60 a duniya, wadda ta ce ƴan bindigan sun saketa ne a sakamakon rashin lafiya da take fama da shi.

An yi garkuwa da matafiya a cikin jirgin ƙasa ne a ranar 28 ga watan Mayun shekarar da mu ke ciki.

Sai dai sun saki wasu daga cikin fasinjojin daga bisani.

Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta sha alwashin tsayawa tsayin daka don ganin an kuɓutar da fasinjojin daga hannun ƴan bindigan.

Ko a kwanakin baya sai da hukumar ta dakatar da jigilar fasinjojin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Legas sakamakon hari da ƴan bindigan su ka kai wa wasu fasinjojin a hanyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: