Gwamna Ganduje Ya Taya Shugaban Karamar Hukumar Ungogo Ramat Murna Kan Zabensa Daya Daga Cikin Matasa 50 Mafi Muhimmanci A Afirka.

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya taya Shugaban Karamar Hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat murnar kasancewa daya daga cikin matasa 50 masu muhimmanci a nahiyar Afirka. Duba da yadda suke kawo cigaban al’umma musamman ta yin amfani da hanyoyin zamani na sadarwa.
An yi bikin ba su kyaututtukan girmamawa a Dubai, wanda Injiniya Ramat tare da ragowar matasan su ka karbi shaidar girmamawa daga Masaraucin Dubai, wato Sheikh Rashid Bin Majid Al-Mu’alla.

Maigirma Gwamna ya ce “Kamar yadda kungiyar nan ta Matasan Afirka mai suna Pan African Youth Leadership Foundation ta zabi Shugaban Karamar ta Ungogo Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya kasance daya daga cikin matasa 50 da su ka yi fice wajen kyautata rayuwar al’umma a wannan nahiyar ta mu, mun kara tabbatar da cewa shi din abin koyi ne kuma abin alfahari ne gare mu.”

Ya kara da cewa, Ramat kasancewarsa matashin da ya san abinda ke damun ‘yan uwansa matasa kuma har ya ke hobbasa wajen ganin ya samar musu da abubuwan da za su kyautata rayuwarsu, ya cancanci yabo. Kuma ya cancanci ya zama abin koyi.
Wannan gagarumin abu, kamar yadda ya ce, “…ba wai abin a yaba ba ne kawai, a’a abu ne da kuma yake nuna mana irin matakin da Ramat ya taka na kyautata harkar shugabanci a matakin da ya taka. Wannan kuma babban abin a yaba ne.”
“Mun kuma yaba da rawar da yake takawa wajen kyautata harkokinsa na mulki a dukkan bangarorin da a kai amfani da su har ya samu ya kai wannan matsayi,” in ji Gwamnan.
Sannan ya kara da cewa, “Bangarorin kuwa sune samar da zaman lafiya tsakanin al’umma, bin sababbin hanyoyin zamani don kawo cigaba ga al’umma, yin kokarin ganin an kara kyautata hanyoyin samun nasarar cin ma manufa na Muradun Karni (SDGs) da kuma kara kyautata yadda mulkin dimukiradiyya yake.”
“Mu na taya ka murna Injiniya Abdullahi Garba Ramat samun wannan yabo da fice da ka yi a cikin matasan Afirka. Ba wani abu irin wannan ke nunawa ba, face yadda kake samar da ci gaba ga al’umarka da kuma yadda ka dauki matasa da muhimmanci a abubuwan ka na yau da kullum. Ba kuma kawai a Kano ba ko kasar ta mu, har ma a nahiyar Afirka,” in ji Gwamna Ganduje.
Gwamnan ya yi kira ga matasa daga bangarorin nahiyar ta Afirka da su yi koyi da Injiniya Ramat. Sannan kuma Gwamna Ganduje ya ji dadin yadda Ramat ya bayyanawa Al-Mu’alla yadda matasa a Kano ke samun jagoranci na gari daga wajen gwamnan.
Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano
Asabar, 13 ga Agusta 2022
fatimanbaba1@gmail.com
cps@kanostate.gov.ng