Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ta fara shirye-shiryen haramta wa ‘yan kasashen waje sayan amfanin gona a cikin gonakin manoman Najeriya.

Ministan ma’aikatar cinikayya da zuba hannun jari na Najeriya Otumba Adeniyi Aebayo shi ne ya sanar da hakan a yayin kaddamar da wani kwamitin a Abuja.

Adeniyi ya ce gwamnatin tarayya ta amince da matakin hakan a yayin zaman majalisa.

Ministan ya kara da cewa ya zuwa yanzu gwamnatin ta fara shirye-shiryen kaddamar da tsarin noma da kiwo.

Adeniyi ya ce gwamnatin na kokarin samar da kyakkyawan yanayi ga wadanda su ke son sayen amfanin gona.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin ta dauki matakin hakan ne domin kawo karshen kalubalen da ake fuskanta a fannin aikin noma tare da bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Adeniyi ya kuma ce gwamnatin ta ce hakan ne zai kawo karshen yadda ake tauyewmanoma wajen samun riba a amfanin gona wanda ya kama su samu domin sayan kayan da za su yi amfanin gona da shi.

Ministan ya nuna rashin jindadin sa akan yadda ‘yan kasashen waje su cutar manoma a Najeriya wajen sayen kayan da su ka shuka a gonakin su.

A jawabin shugaban kwamitin Sulaiman Audu ya bayyana cewa kwamitin nasu zai yi aiki tukuru yadda ya kamata akan abinda ya sa gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: