Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta kama wasu fasinjoji biyu da bindigogi guda 12 da kuma harsasai 374.

An kama mutanen ne jiya Juma’a a jihar Kogi.
Shugaban hukumar ta NDLEA reshen Jihar Kogi Abdulkadir Abdullahi Fakai ya bayyana cewa jami’an hukumar sun kama mutanen a lokacin da su ke tsaka da gudanar da sintiri akan titin Okene Lokoja zuwa Abuja.

Kamfanin dillancin labarai a Najeriya NAN ya rawaito cewa fasinjojin sun hada da Bello Shehu Usman da Sagir Isyaka kuma sun kama su ne a mota kirar J5 inda su ka nufi shiga garin Abuja.

Kwamandan ya ce mutunen masu shekaru 40 da 42 sun tafi ne a cikin mota J5 daga Onitsha zuwa garin Abuja.
Fakai ya kara da cewa bayan tsare su da jami’an su ka yi su na binciken jakun-kunan su, su ka yi arba da makaman.
Shugaban ya ce bayan samun kayan laifin su ka aike da su ga jami’an ‘yan sanda domin fadada bincike akansu.