Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta sake tabbatar da wani sabon hadarin Kwale-kwale a cikin karamar hukumar Ringim ta Jihar.

Jami’in hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sanda Jihar SP Lawan Shisu Adamu ya tabbatar da hakan a garin Dutse babban birnin Jihar.

Shisu Adam ya bayyana cewa lamarin ya farune a jiya Lahadi inda su ka samu labarin faruwar lamarin da misalin karfe 12:40 na rana.

Kakakin ya ce jirgin na dauke da mutane 13 wanda su ke kan hanyarsu ta zuwa Gaisuwa mutuwa.

Lawan Shisu ya kara da cewa Jirgin ya taso ne daga kauyen Dabi zuwa Siyangu da ke karamar hukumar ta Ringim.

Kakakin ya ce su na kyautata zaton hadarin ya farune sakamakon karo da jirgin na Kwale-kwale yayi da wani abu.

SP Lawan Shisu Adam ya ce bayan samun faruwar lamarin inda su ka aike da jami’an su tare da tallafin masunta domin ceto mutanen.

SP Lawan ya kara da cewa ya zuwa yanzu sun ceto mutane bakwai inda su ka aike da su zuwa Asibiti domin kula da lafiyar su.

Kakakin rundunar ya ce biyu daga cikin mutanen mai suna Lubabatu mai shekaru 30 da Muhammad Surajo mai shekara uku sun rasa rayukan su.

Shisu ya kara da cewa bayan mutuwar mutanen sun mikasu ga ‘yan uwansu domin yi musu sutura.

Kazalika ya ce saura mutanen kuma har yanzu su na ci gaba da neman su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: