Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wata mata mai shekaru 25 mai dauke da tsohon ciki da yin safarar miyagun kwayoyi a garin Auchi da ke Jihar Edo.

Mai magana da yawun hukumar a Najeriya Femi Babafemi ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a birnin tarayya Abuja.

Babafemi ya ce jami’an hukumar sun kama matar ne a ranar juma’a kuma sun kamata dauke da nau’in magungunan ruwa masu sinadarin Codeine da kuma wiwi.

Femi ya kara da cewa a makonnin da su ka gaba jami’an hukumar sun kama masu safarar miyagun kwayoyi a Jihohin Legas Gombe da kuma Kogi.

Babafemi ya kara da cewa a wani bincike da jami’an su ka gudanar a Jihar Legas wanda su ka yi yunkurin zuwa kasar Amurka da Australia sun kama mutane tare da dakile tafiyar.

Ya ce kwayoyin da aka kama sun an boye su ne a jikin hannun jakunkuna suturu gari da kuma sauran wasu gurare da aka boye kwayoyin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: