Jami’an rundunar sojin Operation hadin kai sun kai wa mayakan boko haram wani harin kwanton bauna a jihar Borno.

Jami’an sojin sun kai harin ne a yankin kasuwar Daula da ke cikin karamar hukumar Bama ta Jihar.

Jami’an sun kai wa mayakan harin ne bayan wasu bayanan sirri da su ka samu a lokacin da mayakan su ke kan hanyar su ta dawowa daga kasuwa bayan kammala harkokinsu.

Sojin wanda su ke gudanar da sintiri bayan samun bayanai a kansu su ka yi musu kwanton bauna kafin su karasa.

Bayan isar mayakan boko haram su ka bude musu wuta inda su ka hallaka bakwai yayin da daya ya tsere.

Mai sharhi akan sha’anin tsaro Zogazola makama ya gano cewa wanda ya tsere daga cikin wanda aka hallaka ya je gurin babban kwamandan kungiyar su mai suna Abu Hassana inda ya shaida masa cewa an hallaka masa yara.

Zogazola ya ce bayan shaida masa da daya daga cikin ‘yan kungiyar yayi kwamandan ya hada kan sauran yaran nasa tare da nufar garin Bama da nufar kai hari akan dakarun bataliya ta 21.

Makama ya kara da cewa bayan isar mayakan garin na Bama da su ka yi su ka fara harbe-harbe inda hakan ya tayar da hankunan al’ummar yankin.

Zogazola ya ce bayan isar mayakan jami’an sojin da ke zaune cikin shiri su ka bude musu wuta wanda hakan ya tilasta musu tserewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: