Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar.

Hutun da gwamnatin ta bayar ta yi ne domin murnar zagayowar ranar samun ƴancin kai a Najeriya.

Gwamnatin ta sanar da hutun ta bakin ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola wanda babban sakataren ma’aikatar Dakta Shu’aib Belgore ya sanyawa hannu.

Ministan ya taya al’ummar Najeriya murna a bisa zagayowar ranar samun ƴancin kai wanda ya kama ranar Asabar 1 ga watan Octoban shekarar da mu ke ciki.

Sannan gwamnatin ta buƙacin haɗin kan ƴan Najeriya wajej ganin an haɗa kai domin tunkarar ƙalubalen da ƙasar ke ciki.

Gwamnatin ta buƙaci ƴan ƙasar da su yi amfani da ranar samun ƴancin kai wajen nuna alhini da irin yanayin da ƙasar ke ciki wajen murnan samun ƴancin kai.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: