A kalla mutum 101 ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne kuma ake tsammanin sun tsere daga gidan yarin Kirikiri dake jihar Legas.

Kamar yadda shafin yanar gizo na wata gidauniyar bincike ta bayyana, ma’aikatan gidan yarin sun bude musu hanya tare da sakinsu suka kama gabansu duk daga cikin yarjejeniyar sakin sauran fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wadanda aka sace a ranar 28 ga watan Maris.
Majiyar tace wadanda aka saki duk suna jiran a kammala shari’arsu ne wacce aka fara a 2009 kuma dukkansu sun san batun balle magarkamar Kuje da ‘yan ta’adda suka yi tun kafin lamarin ya faru.

A sirrance suka saki mutum 101 da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne wurin karfe 6 na safe a cewar binciken.

Wata majiya tace an kwashe watanni ana yarjejeniyar, tare suke sallah da su kuma a yayin da suke wurin sallah ne suka sanar da shi cewa zasu tafi gida a watan Oktoba.
Sai dai wani jami’i a gidan yarin ya musanta wannan ikirarin.
Majiyar tace ana ta kokarin sakin wadanda ake zargin ne saboda yadda aka tsare su ba bisa ka’ida ba.
An yi kokarin zantawa da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali kan lamarin amma har yanzu ba a samu dama ba.