Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC Bola Tinubu ya sha alwashin hako man fetur a Arewa da kuma inganta tsaro muddin aka zabe shi a shekarar 2023.

Tinubu ya ce zai hako arzikin mai da Najeriya ke da shi a Binuwai da yankin Tafkin Chadi, kana ya bai wa fannin tsaro muhimmanci don amfanin al’ummar kasa.

Dan takarar ya sha alwashi ne yayin da yake jawabi a wajen taron da wasu kungiyoyin Arewa suka shirya ranar Litinin a Kaduna.

Kungiyoyin sun shirya taron ne domin jin irin burin da ƴan takarar ke da shi na bunkasa Arewa idan Allah Ya ba su mulkin kasa.

A cewar Tinubu, akwai tarin arzikin fetur da iskar gas a Binuwai da yankin Tabkin Chadi da sauran wurare a Arewacin kasar.

Ya ce aikin samar da gas din zai taimaka ainun wajen kafa masana’antu a yankunan da kuma tara kudin shiga don amfanin kasa.

Kazalika, dan takarar ya yi alkawarin karasa aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano da kuma aikin shimfida bututun gas da ake kan gudanarwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: