Helikwatar tsaro a Najeriya ta tabbatar da cewar harin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu ɗari a Najeriya.

Babban hafsan tsaron Najeriya Lucky Irabo ne ya tabbatar da haka a Abuja wajen taron bitar ayyukansu.

Ya ce sama da mutane miliyan biyu aka raba da muhallinsu a sanadin hare-haren mayaƙan.

Sannan an samu asarar dukiyar da ta kai tiriliyan 3.24 wadda ta lalace a sanadin rikicin.

Sai dai ya ce a wannan lokaci an ɗauki gaɓar magance matsalar tare da kawo ƙarshenta baki ɗaya.

Domin magancee matsalar tsaron, helikwatar tsaro ta karɓi kuɗin da ya kai naira tiriliyan 2.5 a tsakanin shekaru bakwai.

A halin yanzu, rundunar tsaron na akin daƙile aikin masu satan ɗanyen mai a yankin Neja Delta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: