Fitacciyar malamar addinin musulunci a Najeriya Malama Fatima Nabulisi Baƙo MFR ta zama shugabar Mujallar Matashiya ta aƙalla mintuna goma.

Malamar ta karɓi ragamar jagorantar gidan talabijin yayin ziyarar jaje da ta kawo ofishin Mujallar Matashiya ranar Laraba.

Malama Tasalla ta jajantawa shugaba Abubakar Murtala Ibrahim da sauran ma’aikata da ƴan jarida da sauran al’ummar gari bisa waani yunƙuri da wani soja ya yi na hallaka shugaban ranar Alhamis.

Malama Fatima Baƙo MFR ta yi addu’ar Allah ya kiyaye gaba tare da fatan za a zurfafa bincike domin kamo sojan da ya yi yunƙurin hallaka shugaban.

Ziyarar wadda ta samu rakiyar shugaban ƙungiyar matasa arewacin Najeriya Alhaji Ɗahiru Nabulisi Baƙo da sauran mambobin ƙungiyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: