Rundunar ƴan sanda a jihar Zamfara ta kuɓutar da mutane 27 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na jihar.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar Muhammad Shehu ya rabawa manema labarai ranar Asabar.

An yi garkuwa da mutanen a ƙauyukan Akawa, Gwashi, Tungar Rogo da wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Anka.

Ƴan bindigan sun girke mutanen a wasu dazuka da ke ƙananan hukumomin Bukkuyum da ƙaramar hukumar Anka a jihar Zamfara.

Ƴan sanda sun fra samun bayanai a kan yin garkuwa da mutanen tare da tafiya da su dazukan Bando, Bagega, da dajin Sunke.

Tun bayan kuɓutar da mutanen an kai goma daga cikinsu zuwa asbiti domin duba lafiyarsu yayin da aka garzaya da sauran 17 daga ciki zuwa helikwatar ƴan sanda ta jihar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar ya yabawa gwamnatin jihar a bisa haɗin kai da su ke samu domin tabbatar da tsaro a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: