Rundunar sojin samar Najeriya ta samu nasarar kashe babban ɗan bindiga da ya addabi jihar Zamfara da Katsina.

An hallaka Halilu Tubali da wasu mabiyansa a sansaninsu yayin da jami’an sojin saman Najeriya su ka kai musu hari.
Rundunar tsaro a Najeriya ta tabbatarwa da BBC faruwar lamarin wanda aka yi a makon da ya gabata.

Jami’an sun samu labarin ƙasurgumij ɗan bindigan na yin taro da mabiyansa a cikin dajin wanda hakan ya sa hukumomin su ka yi amfani da damar wajen kai musu hari.

Rundunar tsaron ta tabbatar da cewar mutumin da aka kashe na shigo da makamai tare da rabawa ga ƴan bindigan da ke Zamfara da Katsina.
A cewar mai magana da yawun rundunar sojin saman Najeriya Edward Gabkwet jami’an sun lalata wani waje da ƴan bindiga ke ajiye makamai a cikin dajin.
Sai dai babu bayani a kan adadin mutanen da aka kashe.