Jakadan ƙasar Turkiyya a Najeriya Hidayet Bakyraktar ya shaida cewar ƙasarsu na gab da kammala ƙera jiragen yaƙi marasa matuƙi tare da bai wa Najeriya.

Ƙasar Turkiyya za ta taimakawa Najeriya da jiragen yaƙi marasa matuƙi don ganin an tallafawa ƙasar a ɓangaren tsaro.
Kamfanin Dillacin Labarai na ƙasa a Najeriya NAN ya ruwaito cewar, Jakadan ƙasar Turkiyya a Najeriya na wannan bayani ne yayin wani taron bikin ranar Turkiyya da aka gudanar a ofishin jakadancin ƙasar da ke Abuja ranar Asabar.

Ya ce baiwa Najeriya jiragen da ma masu saukar ungulu wani ɓangare ne daga yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin kasashen biyu a shekarar 2021.

Ya sake tabbatar da cewar akwai jiragen yaƙi marasa matuƙi da kuma jirage masu saukar Ungulu da ma na’urar ɗaukar hoto da bidiyo mai tashi sama da ƙasar Turkiyya za ta tallafawa Najeriya.
Sannan kayan yaƙin da za su tallafawa Najeriya ya ce ya na da yaƙini za su taimaka wajen samar da tsaro a ƙasar.
Idan ba a manta ba, Najeriya na fuskantar matsalarr tsaro fiye da shekaru goma wanda aka gaza kawo ƙarshenta zuwa yanzu.