Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci wani taron gaggawa da manyan hafsoshin tsaro na kasa a kan lamarin tsaro.

Kamar yadda mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwar zamani, Buhari Sallau ya sanar a shafinsa na Facebook, taron ya gudana ne a safiyar yau Litinin, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ana sa ran za su sake bita da kuma karfafa lamarin tsaro a kasar nan.

Idan za ku tuna, ofishin jakadancin Amurka ya yi gargadi kan yiwuwar kai hare-hare a wasu yankunan babban birnin tarayya Abuja.

Hakan ya haifar da tsoro da fargaba a tsakanin al’umma domin kasashen Amuruka da Burtaniya sun shawarci yan kasarsu da su bar Abuja.
Sai dai kuma, da take martani kan lamarin, hukumar DSS ta bukaci yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu amma su zamo masu lura.
A wata sanarwa daga kakakinta, Dr. Peter Afunanya, DSS ta shawarci yan Najeriya da su yi taka-tsantsan, sai dai ta bayar da tabbacin cewa za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya.
Hukumar ta bukaci yan Najeriya da su sanar da hukumar bayanai da ke da nasaba da barazana ko ayyukan da basu yarda da shi ba.