Hukumar kula da yanayi ta Nigeria (NiMet) ta sanar da ƙarewar yanayin damina a Arewacin kasar.

Hukumar ta ce za’a sami tasowar ƙura daga jamhuriyar Nijar zuwa kasar Najeriya inda ƙurar za ta mamaye wasu sassa na Arewacin kasar.

Hukumar ta ce iskar mai karfin maki 800 da ake hasashen za ta taso daga ƙasar Nijar za ta mamaye sassan Najeriya ciki har da Arewa ta tsakiya.

Binciken hukumar ya nuna akwai yiwuwar ƙarin hazo a wasu sassan kasar.

A cikin sa’o’i 24 masu zuwa, akwai yuwuwar karin hazo da kura a matsakaicin nisan zango na mita dubu biyu zuwa mita dubu biyar a jihohin Borno, Yobe, Katsina, Kano, Kaduna, Gombe, Bauchi da kuma jihar Jigawa.

Yayin da sauran jihohin Arewa ciki harda Arewa ta tsakiya na iya fuskantar yanayin zafi kan mataki na biyar zuwa mataki na bakwai.

Ana sa ran wannan yanayi zai ci gaba har zuwa kwanaki uku masu zuwa.

Hukumar ta ce yanayin zafin rana zai ƙaru a hankali.

Hukumar ta shawarci masu ababen hawa da su rikayin tuki cikin nutsuwa a wannan yanayi.

Hukumar ta shawarci ma’aikatan jirgin sama da su nemi sabbin rahotannin daga hukumar don inganta ayyukansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: