Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU reshen Jihar Filato ta bai wa mambobin kungiyar umarnin zama a gidajen su harsai lokacin da gwamnatin tarayya ta biya musu dukkan albashin da su ke binta.binta

Shugaban kungiyar na Jami’ar Dr Lazarus Maigoro ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a a garin Jos.

A yayin sanarwar Dr Maigoro ya bayyana cewa sun dauki matakin ne bayan wani zama da su ka gudanar wanda kuma hakan ba ya na nufin sun shiga yajin aiki ba ne.

Shugaban ya ce bayan kammala zaman su ka dauki matakin sakamakon kin biyan su cikakken albashin watan Oktoba da gwamnatin ta ki yi.

Dr Lazarus ya kara da cewa gabanin janyewar su daga yajin aiki sun cimma da matsaya da yarjejeniya da kakakin majalisar wakiai Femi Gbajabeamilia wanda gwamnati za ta biya kashi 50 cikin 100 na dukkan albashin watannin da ba ta biya su ba ba tare da bata lokaci ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: