Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta (EFCC), Abdulrashid Bawa, ya ce dole a kara wa hukumarsa kudade matukar ana so a samu gagarumar nasara a ayyukan da suke yi na dakile cin hanci da rashawa.

Abdurrashid Bawa ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayani a gaban Kwamitin Yaki da Rashawa na Majalisar Wakilai a ranar Talata.

A wata zantawar sa da ’yan jaridu bayan kammala zaman, Abdulrashid ya ce sun bukaci karin kudin ne don makarantar yaki da rashawa ta hukumar da ma sauran ayyukanta na yau da kullum.

Ya ce su na aikin gina sabuwar makarantar yaki da rashawa, kuma su na bukatar kudin kammala ta.

A bara, an ware mata Naira biliyan uku, amma a bana ko sisi ba a warewa makarantar ba.

A game da makarantar da suke ginawa Shugaban ya ce akwai bukatar wannan makaranta saboda akwai kwasa-kwasan da suke son koyarwa don yaki da wadannan miyagun dabi’u na cin hanci da rashawa.

Ya kara da cewa  hanya dayace za ta basu nasara a kan ayyukansu wanda shi ne yawan ba da horo a kai-a kai ga ma’aikatansu.

Sannan ya ce  ya na da kwarin gwiwar cewa majalisar, wacce ya ce tana da kyakkyawar alaka da hukumarsa, za ta amince da bukatar ta su.

Shugaban ya kuma ce hukumar EFCC ta sami nasarar kwato dimbin kadarori daga wadanda suka sace kadarorin gwamnati da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: