Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare ta Najeriya Hajiya Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya za ta daina biyan kuɗin tallafin man fetur a watan Yunin 2023.
Hajiya Zainab ta bayyana haka ne a lokacin taron manema labarai da ya gudanar a Abuja babban birnin ƙasar bayan kammala taron tattalin arziki na ƙasa karo na 28.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga jami’an tsaron kasar da su gudanar da bincike domin gano wadanda suka kashe sarki Obudi Agwa Eze Ignitus Asor da ke jihar Imo.
A ranar Litinin ne dai wasu ‘yan bindiga suka kutsa fadar sarkin inda suka halakashi tare da wasu fadawansa hudu ta hanya bude musu wuta da bingigogi.


‘Yan Najeriya na ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta dangane da wasu kalamai da ɗan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi a wurin yaƙin neman zaɓensa a jihar Filato.
A jiya Talata ne Bola Tinubu ya kaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓen nasa a Jos, babban birnin jihar Filato, wanda Shugaba Muhammadu Buhari da sauran jiga-jigan jam’iyyar suka halarta.
Wasu asu sana’ar canjin kudi su shida sun shiga hannun hukuma , bisa zarginsu satar wani dan abokin sana’arsu.
Ana zargin ’yan cajin sun hada baki sun sace karamin yaron mai shekara takwas a duniya ne a Jihar Legas.
Dan majalisar dokokin Jihar Legas, Hon. Abdulsobur Olayiwola Olawale ya rasu a wajen kaddamar da takarar Tinubu a Jos, babban birnin Jihar Filato.
Marigayin na wakiltar mazabar Mushin II a majalisar dokoki ta Jihar Legas.