Kungiyar ma’aikatan jami’o’i, ASUU, reshen Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa ta nuna kin amincewarta da mayar da ma’aikatanta tamkar na wucin gadi.

Shugaban na ASUU a FUD, Dr Bashir Yusuf ya bayyana hakan yayin zanga-zangan, yana mai cewa hakan ya saba dokokin aiki, da dokokin kwadago na kasa da kasa da aikin gwamnati.

Dr Bashir ya yi bayanin cewa malaman jami’o’in ma’aikata ne da aka dauke su aiki na cikakken lokaci wadanda ayyukansu ke da wasu banbance-banbance da wasu ma’aikatan gwamnati masu zuwa aiki karfe 8 na safe zuwa 4 na yamma.

A cewarsa, koyarwa a jami’a cikakken aiki ne da ya kunshi koyarwa, bincike da ayyukan yi wa al’umma hidima.

Kungiyar ASUUn ta FUD, ta yi tir tare da nuna amincewarta da mayar da malaman ma’aikatan wucin gadi kuma ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta biya su cikakken albashinsu da allawus.

Malaman na FUD sun yi tattaki na lumana daga Cibiyar Dalibai zuwa ginin Majalisar Jami’ar rike da takardu masu dauke da rubutu daban-daban don isar da sakon su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: