Gwamnatin tarayya tace jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna zasu dawo aiki kafin nan da makonni biyu.

Ministan sufuri, Mu’azu Jaji Sambo, ya bayyana hakan a jiya Alhamis a filin jirgin kasa dake Moniya a Ibadan yayin da yaje ziyarar duba wurin karo na farko.
Ya tabbatarwa da fasinjojin jirgin kasa na fadin kasar nan cewa za su kasance masu matukar tsaro a yayin da suka hau jiragen kasan.

Ministan da ya samu rakiyar karamin ministan sufuri, Prince Ademola Adegoroye, manajan daraktan hukumar kula da jiragen kasan, NRC, Fidet Okhiria da sauran jami’an ma’aikatar, yace gwamnatin tarayya ba zata sassauta ba wurin tabbatar da tsaro a jiragen kasan ba.

A cikin makonnin da suka gabata ne aka dinga yada cewa gwamnatin tarayya tace za a dawo da jigilar jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna.
Sai dai kwanaki kadan bayan fitar wannan labarin, gwamnatin tarayya ta fito tare da musantawa, lamarin da yasa murna ta koma ciki ga masu daukin komawa hawa jiragen kasan.