Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta kama mai garin Gobirau da ke karamar hukumar Faskari ta Jihar Surajo Madawaki bisa zargin sa da hada kai da ‘yan ta’adda wajen hallaka manoma.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar SP Gambo Isa ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a.
A yayin jawabin na Gambo Isa ya ce sun kama mutumin ne bayan wani kiran gaggawa da su ka samu ‘yan bindiga sun hallaka wani Yahya Danbai dan shekaru 35 a lokacin da ya ke tsaka da aiki a gonarsa.

Bayan hallaka manomin aka sanarwa da dagacin amma bai kira jami’an tsaro ba.

Kakakin ya ce daga bisani dagacin bayan ya samu bayani ya kira jami’an tsaro sannan ya hada baki da dan bindiga da ya kawo masa bindigar da aka samu daga shugaban ‘yan bimigar.
Kazalika Gambo Isa ya kara da cewa bayan shigar ‘yan bindigan gonar manomin yayi karfin hali wajen kwace bindiga kirar AK 47 daga gurin su tare da kai wa dagacin.
Kakakin ya ce bayan kai wa dagacin bindigar da manomin yayi Dagacin ya kira wani rikekken shugaban ‘yan bindiga mai suna Hamisu ya bashi bindigar da manomin ya samu nasarar kwato wa.
SP Gambo ya bayyana cewa bayan Dagacin ya bai wa dan bindigan Bindigan ya tattaro yaransa inda su ka nufi kauyen da manomin ya ke zaune inda su ka hallaka shi.
Kakakin ya ce ‘yan bindigan sun kuma sanya wa mazauna kauyen harajin naira miliyan goma tare da kafa musu dokar hallaka su matukar basu biya ba.
Ya ce daga bisani Dagacin ya amsa laifin da ake tuhumar sa dashi bayan binciken da aka gudanar.