A wani ƙudiri da Majalisar dokoki ta jihar Bayelsa ta gabatar,cewa a riƙa biyan ƴan majalisu kuɗin fansho bayan kammala wa’adin su na zaman majalisa.
Ɗan majalisa Peter Akpe ne ya gabatar da ƙudurin a zauren majalisar,inda ya bayyana ƙudirin cewa a dinga biyan shugaban majalisa naira dubu 500 duk wata a matsayin fanshon sa bayan ya bar majalisa.
Haka kuma, ƙudirin ya buƙaci gwamnatin jihar ta biya mataimakin shugaban majalisar naira dubu 200 duk wata a matsayin fansho bayan ya bar aiki, a yayin da dokar ta nemi a biya sauran ƴan majalisun naira dubu dari-dari a kowane wata.
Haka zalika dokar ta sa tsofaffin ƴan majalisar jihar a cikin waƴanda za su ci gajiyar ƙudirin sune,
Ƴan majalisun da su ka wakilci al’ummar su kafin samar da jihar Bayelsa sune za su fara amfana da sabon tsarin biyan fansho ga ƴan majalisun.
Sai dai Yanzu, ana jiran gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson da ya sanya hannu a kan ƙudurin don ya zama doka.
Duk da Al’ummar jihar basa goyon bayan wannan ƙudiri.


