Gwamnatin tarayya ta ce an kwato sama da dala biliyan ɗaya da aka sace daga asusun gwamnati tun farkon gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnatin tarayya jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda ya gabata a jiya laraba.

Ya ce an mika kadarorin da aka kwato zuwa sassa daban-daban na tattalin arziki, ciki har da hukumar shirye-shiryen rage radadin talauci, sannan gwamnati ta kama laifuka 109 ne kawai kafin zuwan gwamnatin Buhari, yayin da a gwamnatin Buhari ta yanke wa sama da mutane 3,000 hukuncin a kan laifukan da su ka aikata.

Ya kuma ce majalisar ta amince da sabon kundin dabarun yaki da cin hanci da rashawa na shekarar (2022-2026) don karfafa hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati.

Haka kuma ta amince da cike gibin kasafin kudi na Naira biliyan 14 na aikin babban titin Kano wanda zai hade zuwa Maiduguri da aka baiwa kamfanin Dantata and Sawoe domin gudanar da aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: