Biyo bayan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke da zamanta a jihar Kaduna ta yanke na aminta da sunan Sanata Uba Sani a matsayin dan takarar gwamna a jamiyyar APC da kuma sauran ‘yan takara 34 na mazabun, dan takarar gwamna a jamiyyar NNPP Sanata Suleiman Hunkuyi da kuma jamiyyar sun ce za su kalubalanci hukuncin.

Hunkuyi da jam’iyyar NNPP sun shigar da hukumar zabe ta Najeriya INEC kara bisa sanya sunan dan takarar gwamna na jamiyyar APC Sanata Uba Sani a matsayin dan takarar APC da kuma sauran ‘yan takara 34 na mazabun.
A cikin takardar karar da jam’iyyar NNPP da Hukunyi su ka shigar a gaban kotun, sun ce jam’iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani tare da bin ka’idar zaben ba tare da bukatar kotu ta soke sunayen yan takarar jam’iyyar wajen shiga babban zaben shekarar 2023.

Hunkuyi a wani taron manema labarai da ya yi a Kaduna ya ce, jam’iyyar NNPP ba ta kai karar jam’iyyar APC ko ‘yan takarar gaban kotu ba, illa hukumar zabe da ta ke da allhakin cirewa ko tabbatar da sunan dan takara.

Ya yi nuni da cewa, a mulkin demokiradiyya ana so a yi adalci da kuma gudanar da sahihin zabe, inda ya kara da cewa, jamiyyar NNPP ta dogara ne da sashe na 29 da ke na cikin dokar zabe da aka sabunta wadda ta yi bayani karara cewa, daukacin jamiyyun dole ne su mika sunayen ‘yan takarar su da suka shiga aka fafata da su a zaben fidda gwani.