Wata kotun daukaka kara dake birnin Yola a jihar Adamawa ta tabbatar da Aishatu Dahiru Binani a matsayin halartacciyyar ‘yar takarar gwamnan jihar a karkashin tutar jam’iyyar APC.

Kotun da mai shari’a Tanko Yusuf Hassan yake jagoranta tayi watsi da hukuncin wata kotun tarayya wadda ta soke takarar Aishatu Binani tare da bayyana jam’iyyar a matsayin wadda ba ta da dan takara a babban zaben shekarar 2023.
A lokacin karanto hukuncin, alkalin ya umarci a mika sunan Binani ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a matsayin ‘yar takarar gwamnan ta APC a jihar Adamawa

A baya bayan nan ne dai kotuna daban daban ke sauya hukuncin hukumar zabe ta INEC a kan ‘yan takarkaru daban daban daga jihohi daban-daban a fadin Najeriya.

A hukuncin da Alkalin kotun ya yanke a yau Alhamis ya bayar da umarnin a kai sunan Aisha Binani hukumar zabe ta kasa INEC domin tabbatar da ita a matsayin yar takara a jihar.