Mahukunta a Jamhuriyar Dimokoradiyyar Congo sun ce mutane fiye da 120 ne suka rasa ransu sakamakon mummunar ambaliyar ruwan da aka jima ba a fuskanci irinta ba a babban birnin kasar Kinshasa.

Yawancin wadanda suka rasa ran na su na zaune ne a yankunan da tsaunuka suke inda aka samu zabtarewar kasa.

Rahotanni sun ce akwai iyalan gida guda su tara da suka mutu bayan gidansu ya rufta.

Tuni aka ayyana zaman makokin kwana uku a kasar wanda za a fara daga yau Laraba.

Mutane dai na yawan kaura su koma birnin na Kinshasa, sai dai a shekarun baya bayan nan birnin na fama da rashin magudanan ruwa wanda hakan ke matukar barazana ga mazauna birnin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: