Fitaccen jarumi kuma mai shirya fina finan Hausa TY Shaban, ya sanar da ranar litinin 2/1/2023 a matsayin ranar fara haska sabon film dinsa mai dogon Zango maisuna Lulu Da Andalu.

Shirin Lulu da Andalu shiri ne da zai nuna rayuwa cikin wani salo da siga wadda ba’a saba gani ba, inda za’ayi da rayuwa tsakanin bil’adama da junnu.
Labari ne da ya faru a gaske, shekaru sama da 600 da suka gabata, anyi wani shahararran mai tarin dukiya maisuna MANSA MUSA dan asalin kasar MALI wanda tarihi ya tabbatar da ya taba zama mutumin da yafi kowa tarin dukiya a fadin duniya.

Ya shimfida mulkinsa a matsayin MANSA na MALI tsakanin shekarar 1312 zuwa shekara ta 1337.

Shekaru daruruwa da suka shude an binne wani kaso na dukiyar Mansa Musa a wani guri da babu wanda ya sani sai wasu hatsabiban Aljanu guda biyu, LULU DA ANDALU
TY Shaba ya cigaba da cewa Kwatsam a wannan karni sai aka samu wani bawan Allah wanda burinsa shine ya gano inda dukiyar MANSA MUSA take domin ya mallaketa.
TY Shaba ya kara da cewa Shirin Lulu da Andalu ya ban bata da sauran fina finai masu dogon zango da ake nunawa a yanzu, domin yanayin labarin da ban ne, inda ake daukar shirin na daban ne, Jaruman shirin na daban ne, haka kuma kayan aikin na musamman ne.
Mashiryin film din Lulu Da Andalu TY Shaban ya bayyana cewar sun shirya shirin ne bayan bibiyar tarihi, domin nunawa jama’a yadda alaƙar mutane da aljanu take tun a shekarun baya.
Film din Lulu Da Andalu ya samu aikin bayar da umarni daga Kamilu Ɗan Hausa, Wanda shima yace wannan aikin ya ƙunshi sabbin hanyoyi na zamani wanda za su ƙayatar da masu kallo.
Za’a fara nuna shirin daga ranar litinin 2 ga watan janairun shekarar 2023 a DSTV Afrika Magic Hausa da karfe 7:30 na dare, ya yinda zaku iya kallon wannan film da karfe 8 na dare a manhajar YouTube maisuna TY Shaba TV.
Daga wanann lokaci za’a cigaba da kallon film din a duk kanin ranakun litinin idan Allah ya amince.
Muna dakon sharhi da tambayiyinku da zarar kun fara kallon shirin Lulu Da Andalu daga kamfanin BlueSound and Multimedia