Yan bindiga sun kai hari kan tawagar tsohon gwamnan jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, Ikedi Ohakim, tare da kashe ‘yan sanda huɗu.

Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne a garin Oriagu da ke yankin ƙaramar hukumar Ehime Mbano a jihar, a lokacin da tsohon
gwamnan ke kan hanyarsa ta dawΥowa daga wata ziyara da ya kai tare da ‘ya’yansa biyu.

Mista Ohakim ya tsallake rijiya-da baya yayin harin, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan sanda huɗu da ke cikin tawagar tasa.

‘Yan bindigar sun lalata ɗaya daga cikin
kotocin tawagar tsohon gwamnan, bayan da ba su samu damar kama tsohon gwamnan ba, kamar yadda rahotonni suka bayyana.
Mista Ohakim ya riƙe muƙamin gwamnan jihar daga shekarar 2007 zuwa 2011.