Dan takarar gwamnan a jam’iyyar NNPP a Jihar Katsina ya bayyana cewa baya samu nasarar a zaben shekarar 2023 zai kaba gwamnati bisa tsarin addinin musulunci.

Dan takarar ya bayyana hakan ne a gurin taron al’umma na ‘yan takarar gwamnan a Jihar wanda kamfanin jaridar Daily Trust ta shirya a ranar Asabar.

Dakta Rabe Darma ya ce matukar ya kafa gwamnati a akan tsarin musulunci a shekarar 2023 cin hanci da rashawa ya kare a Jihar ta Katsina.

Ya kara da cewa zai kuma tabbatar da lalubo hanyoyin samun kudaden shiga wanda hakan zai sanya Jihar ta daina dogaro da kasafin kudin tarayya.

Dan takarar ya bayyana cewa za su kafa gwamnatin ne karkashin koyarwar Annabi Muhammad S,A,W da alkur’ani wanda hakan zai magance damuwar da kasar ta ke fama dashi.

Mediya Trust ta shirya taron ne tare da hadin gwiwar raya Demokuradiyya CCD.

Leave a Reply

%d bloggers like this: