Gwamnatin Jihar Neja ta snya dokar hana fita sakamakon hallaka wani basareka da aka yi a Jihar.

Lamarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar sakamakon wata hatsaniya da ta hadashi da wasu matasa.
Ana zargin matasan da hallaka basaraken mai suna Muhammad Abduksafur da ke garin Lambata a karamar hukumar gurara a Jihar bayan jikkata da yayi a lokacin rikicin.

Rahotanni sun bayyana cewa ba a san dalilan hallaka basaraken da matasan su ka yi a cikin gidan sa ba.

Bayan samun rahotan kisan basaraken gwamnatin Jihar ta sanya dokar zaman wanda ba a san ranar cire dokar ba.
Sanya dokar ta zuwa ne ta cikin wata sanarwa da Sakataren gwamnatin Jihar Ahmad Ibrahim Matane ,inda ya ce dokar za ta fara aiki ne da misalin karfe 6:00 na safiya zuwa 6:00.
Sakataren ya kara da cewa matakin hakan zai taimaka matuka wajen bai wa hukumomin tsaro damar tabbatar da zaman lafiya da tsare rayukan mutane tare da dawo da doka da oda.
A cikin sanarwar gwamnatin ta bukaci al’ummar yankin da su bai wa jami’an tsaro hadin kai domin da dawo da ingantacciyar zaman lafiya a garin Lambata.