Hukumar kidaya ta Najeriya wato NPC ta sanya ranar 29 ga watan Maris din shekarar da mu ke ciki a matsayin ranar da za ta gudanar da kidayar al’ummar tare da gidajen su a kasa baki daya.

Shugaban hukumar Nasir Kwarra ne ya tabbatar da hakan a yayin wata ganawa da manema labarai bayan kammala wata ganawa da Shugaba Buhari a fadar sa da ke Abuja ranar Juma’a.
Kwarra ya ce a yayin kidayar hukumar ta NPC za ta kidaya harma da wadanda ba ‘yan Najeriya ba, tare da inganta aikin na kidayar.

Kafin kidayar rahotanni sun bayyana cewa yawan ‘yan Najeriya a yanzu ya haura miliyan 200.

Kwarra ya ce daga ranar 29 ga watan na Maris 2023 zuwa ranar 2 ga watan Afrilu ma’aikatan da hukumar ta dauka za su iya tsintar kansu a cikin yin kidaya.