Gwamnatin Najeriya ta musanta yin karin farashin man fetur, duk kuwa da cewa farashin man tuni ya karu a fadin kasar.

Kafafen yada labarai a Najeriyar sun ambato cewa karamin ministan albarkatun man fetur na kasar Timipre Sylva a wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a, ta hannun mai taimaka masa kan kafofin yada labarai, cewa shugaban  kasar bai amince da wani Karin sabon farashi ga man fetur din ba.

A ranar Juma’ar ne dai shugaban masu gidajen mai masu zaman kansu reshen jihar Kano, Bashir Danmallam ya tabbatarwa da BBC  karin farashin man fetur din da kashi 8.8 cikin 100, inda ya ce sun samu umarni ne daga gwamnatin tarayya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa babu wani dalili da zai sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da karin farashin mai a daidai wannan lokaci.

Haka-zalika sanarwar ta tabbatar da cewa gwamnati ba za ta amince da karin farashin man fetur a asirce ba, ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki a fannin man fetur ba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: