Shugaban hukumar dakile cututtuka  masu yaduwa a Najeriya  NCDC ya bayyana cewa barkewar cutar murar mashako a wasu sassan kasar nan ba abu ne da zai daga wa yan kasar hankula ba.

Kalaman na Dakta Ifedayo Adetifa na zuwa ne bayan da aka samu rahoton mutuwar mutum 25 a jihar Kano sakamakon kamuwa da cutar ta Mashako yayin da aka samu rahoton cewa mutane  33 sun kamu da cutar a wasu sassan kasar ciki har da jihar Lagos.

Hukumar ta NCDC ta ce tana lura da mutanen da ake tsammanin sun kamu da cutar tare da bayar da shawara ga jama’a da su tabbatar da cewa sun karbi allurar rigakafin cutar musamman ma kananan yara.

An bayyana cewa ana daukar cutar ne dai ta hanyar tari da hada numfashi na mai dauke da ita, ko ta hanyar amfani da wasu abubuwa da mai dauke da cutar ya yi amfani da su, kamar kofin shan ruwa ko cokali ko tufafi ko ma kwanciya waje daya da mai dauke da cutar.

Dakta Adetifa ya ce bai kamata yan Najeriya su daga hankalinsu kan barkewar cutar ba, saboda akwai wadatattun magunguna da rigakafin da za su magance cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: